Yadda taron Majalisar mata ya gudana a karamar Hukumar Kura.

Kungiyar majalisar mata ta kasa CT reshen jihar Kano a cigaba da kewayan da take yi na kananan hukumomi 44 dake jihar Kano a Jiya ta gudanar da taron a karamar Hukumar Kura inda uwar gidan shugaban karamar Hukumar Hajiya Laywisa Tijjani Mustafa Abdullahi Rabiu ta tarbe su.

Hajiya Lawisa ta yabawa da Kuddirinta kungiyar kuma zata Cigaba Da jajircewa domin ganin kungiyar ta Kasa musamman Reshen Jihar Kano ta sami Goyon Baya  Kowanna Bangare Musamman Ta Wajan Wayar Da Kan Mata  Illolin Shan Miyagun Kwayoyi Da Inganta Rayuwar su.

Tun da fari Shugabar Kungiyar ta kasa reshen jihar Kano Hajiya Amina Shehu Ismail Bunkure tace Manufar kungiyar shine shiga lungu da sako domin wayar da kan Mata Illolin Shaye-Shayen Miiyagun Kwayoyi, da Nemawa Mata Mafuta Wajan
Inganta Rayuwarsu Dan Cigaban Walwalarsu

Amina tace a cigaba da kewayen da suke na kaddamar da shugabanci a kananan hukumomin jihar Kano, Kura, itace ta 43 kuma suna sa ran zasu karkare kewayen da karamar Hukumar Dawakin Kudu.

Daga karshe ta yabawa gwamnatin jihar Kano bisa jajircewar da take wajan tallafawa rayuwar mata kuma yaba da tarbar da kungiyar ta samu daga mai dakin shugaban karamar Hukumar Kura Hajiya Lawisa Tijjani.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments