Wata kotun majistare da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta bada umurnin tasa keyar Farfesa Zainab Duke Abiola zuwa gidan yarin Suleja bisa zargin cin zarafin Teju Moses, yar sanda mai tsaronta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kotun Ta Tura Farfesan Da Ta Yi Wa ‘Yar Sanda Mai Tsaronta ‘Jina-Jina’ Gidan Yari.
A wani bidiyo da ya bazu a ranar Laraba, an ga yar sandan zaune a kasa tana bukatar a kai ta asibiti yayin da jini ke zuba daga jikinta.
Yan sanda sun zargi Abiola, lauya kuma mai rajin kare hakkin bil adama, ta yunkurin aikata kisa da cin zarafi da gangan Dan cin amana.