A P C ta cire sunayen wasu jigajigan jam’iyar daga cikin yakin neman zabe Tinubu
Kawo Yanzu majiyar zartarwa ta yakin neman zabe a jam’iyar APC ta fitar da sunayen mutane 422 da zasu jagoranci yakin neman zabe na Dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.
A sabuwar Sanarwar da majalisar kolin yakin neman zabe ta fitar a Abuja ta bakin mai magana da yawun ta James Falken, ya nuna wasu gyare-gyare da majalisar tayi.
A sabon lis din da majalisar yakin neman zaben ta fitar a Daren Jiya gwamnan jihar filato ya rasa muKamin sa shugaban yakin neman zabe inda ya dawo mataimaki
Kazalika Sanarwar tace wasu jigajigan jam’iyar suna yaki da kudurin Tinubu na hada musulmi da musulmi in da ya dauko matakin sa daga jihar Borno.
Kana wasu daga cikin wadanda aka kara baiwa mukamai sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da tsohon sifika Yakubu Dogara; da tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal; da tsohon Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba da kuma shugaban kungiyar Tinubu-Shettima Coalition for Good Governance Adebayo Shittu.