Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen malam kato,ta bayyana godiyarta ga Gwamnatin da Hukumar kula tsara birane da karkara na jihar kano,bisa yunkurinsu na dawowa da alummar da suka rasa guraren sana,oinsu dake cikin Tashar ta Malam Kato.
Shugaban kula da binciken kudade na Kungiyar Alh Samaila Giredi ne,ya tabbatar da haka a lokacin da kungiyar ta shirya taron manema labarai, dangane da gine_ginen da wasu mutane suke yi ba bisa kaida ba.
Yace, sakamakon gine ginen da aka yi,ya sanya Dumbum jama,a sun bar guraren da suka cin Abinci a cikin Tashar,wadanda Akasari magidanta ne,inda yace, bayyana direbobi akwai masu harkar kasuwanci.
Samaila yace,bisa hakan ne kungiyar ta Nuna farin cikinta saboda tsayar da ginin da wasu masu hannu da shuni suke yi, Wanda ya farune gaf da Gwamnatin da ta gabata za ta Tafi.
Shugaban yace, sai dai kuma Allah ya tausawa bayin Allah da suke Neman abincinsu a Tashar, Bisa tausayi da hangen nesa da Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf take da shi na taimakawa Wanda aka zalunta.
Ya kuma bayyana cewa, Kungiyar Direbobin,ba za ta gajiya ba wajen bin dokokin da Gwamnati da masu ruwa da tsaki akan wannan lamari domin ciyar da jihar kano gaba,musamman ta fannin sana,ar Yankungiyar wato,Harkokin Tuki.
Yace, za su yi amfani da wannan dama wajen baiwa Gwamnatin tabbacin domin hada hannu na Samar da kudade shiga Wanda da sune Gwamnati take ayyukan ci gaba da za su taimaki Alumma.
Haka zalika,ya bukaci yankungiyar Tashar ta Malam Kato,da su kara himmatuwa wajen baiwa Gwamnatin jihar kano hadin kan suka kamata da ma ita kanta Kungiyar Direbobin,Wanda yin zai haifar da ‘Da’ mai ido da bunkasa harkokin sufuri da Samar da ayyukan yi ga matasan da basu aiki a fadin jihar nan.
Yace, yanzu lokaci ya yi da ya kamata kungiyar ta ba da gagarumar gudunmawa ga Gwamnatin da hukumomin kula da harkokin sufuri na jihar kano, domin jihar ta yi gogayya da sauran kasashen ketare da suke habaka bangarori daban daban, musamman bangaren da suka shafi Tuki.
Ibrahim sani gama pyramid radio.