Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce tana sa ido kan gwamnonin ƙasar uku sakamakon yunƙurinsu na halasta kuɗin haram da biliyoyin kuɗin da suka tara ta hanyar biyan ma’aikata albashi a hannu – maimakon ta banki.
Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa yan jarida cewa dakarunsa za su ci gaba da kai samame kan ‘yan canji game da zargin ɓoye dalar Amurka wanda hakan ke sa darajarta na hauhawa.
Duk da cewa Bawa bai faɗi sunan gwamnonin ba, ya ce biyu daga cikinsu daga arewacin Najeriya suke, inda ɗayan yake a kudanci.
Ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa gwamnonin sun kammala shirin fito da kuɗin ta hanyar biyan ma’aikatansu na jiha da garin kuɗi maimakon ta banki kamar yadda aka saba.
Da aka tambaye shi ko EFCC za ta yi wa gwamnonin sammaci, Bawa ya ce suna dai saka musu ido zuwa yanzu.
Wasu masana na ganin cewa hakan na da nasaba da ƙarin karyewar darajar nairar. CBN ya ce za a fara amfani da sabbin takardun kuɗin daga ranar 15 ga watan Disamban 2022.