Shugaban Amurka zai yi afuwa ga masu laifin ta’ammali da wiwi.
Daga Walid Hari
Shugaba Joe Biden na Amurka zai yi afuwa ga duk wani Ba’amurke da kotunan tarayyar kasar suka samu da laifin mallakar wiwi.
Afuwar za ta shafi waɗanda aka samu da laifi ne kawai a ƙarƙashin kotunan tarayya kuma Mista Biden ya buƙaci gwamnonin jihohi da su bi sahunsa wurin ɗaukar irin wannan mataki.
Tuni ƴan Jam’iyyar Republican suka soma caccakar wannan mataki na yin afuwa ga kusan mutum 6,500 inda suka ce wannan wani yunƙuri ne na kawar da hankalin jama’a daga irin gazawar Biden a mulkinsa.
Kaɗan ya rage sanarwar ta Shugaba Biden ta halasta ta’ammali da wiwi, kamar yadda ya yi alƙawari lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.