IDON AMFANIN GONA YA ZO kasuwa tafi tumbatsa. Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi.
Shugabancin kungiyar kasuwar Abinci ta Dawanau, ya sha alwashin bijiro da managartan ayyuka da wayar da kan kananan da Mayan yankasuwa domin sanin kasuwanci a zamanance wajen ganin an bunkasa harkokin kasuwanci da ci gaban tattaliñ arzikin jihar Kano da ma kasa baki daya.
Shugaban kungiyar kasuwar Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi ne, ya bayyana haka ga manema labarai a zantawarsa da su a ofishinsa dake kasuwar anan Kano.
Yace, kungiyar kasuwar da hadin gwiwar hukumomin kula da fitar da kayayyaki da shigowa da su,suna ta tattaunwa wajen ganin an bijiro da hanyoyin da za su baiwa yankasuwa damar fitar kayayyaki da ake samarwa na cikin gida zuwa kasashen ketare yadda za su inganta kasuwancinsu cikin sauki tare da samun riba mai amfanu.Inda yace,wannan wata hanyace da zata kara kawowa Najeriya ci gaba ta fannin kasuwanci.
Kwamaret Rabiu, ya bukaci hadin kan yankungiyar kasuwar wajen aiwatar da shirin,Wanda yace,bayan wannan akwai tsare_tsare na ci gaba da kungiyar kasuwar take kokarin bijiro da su,kuma, za su taimakawa alumma da dama ta hanyar Samar da ayyukan yi ga Matasa da sauran alummar jihar Kano ta fannoni da yawa da kuma,yadda Gwamnati za ta samu kudaden shiga domin bunkasa harkokin tattalin arziki.
Haka zalika,Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi, ya shawarci yankungiyar kasuwar da su,ci gaba da gudanar da addu,oin da za su taimaka wajen ganin kasuwar da alamuranta sun kara habaka yadda yakamata, ta yadda za ta yi gogayya da sauran manyan kasuwannin kasashen Afurika.
Ya godewa Gwamnatin tarayya da ta jiha, bisa yadda suke tallafawa harkokin kasuwanci da fannin Noma,musamman wannan lokaci na Damina da muka shigo.
Ibrahim Sani gama.