Sabuwar shekara NLC ta fitar da Sako ga gwamnatin tarayya

Ƙungiyar ƙwadago ta fitar da saƙo yayin da ake shirin shiga sabuwar shekarar 2025 bayan zuwan ƙarshen 2024

Shugaban ƙungiyar ya buƙaci gwamnatoci a dukkanin matakao su ba da fifiko kan walwala da jindaɗin ƴan Najeriya

Ƙungiyar ta NLC ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta janye kuɗirin harajin da ta gabatar a gaban majalisa

Joe Ajaero, ya ce ƙungiyoyin ƙwadago za su zage damtse wajen neman ƙarin albashin ma’aikata saboda rage tsadar rayuwa.

“Muna kira ga gwamnati a kowane mataki da ta tabbatar da cewa mulki ya zama abin da zai amfani jama’a. Jindadin ƴan kasa ya kasance shi ne dalilin farko na kasancewar kowace gwamnati.”

“Samun abinci mai gina jiki, ingantacciyar kiwon lafiya, gidaje masu inganci, ilmi, sufuri da ƙarin tsaron rayuka da dukiyoyi gami da yancin shiga cikin yanke shawara kan yadda ake mulkarsu shi ne babban abin da mutane da ma’aikata ke fata.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments