FCT, Abuja – Tsohon hadimin shugaban kasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya yi magana kan salon mulkin shugaba Bola
Tinubu. Fitaccen dan siyasar, Femi Ojudu ya Tinubu ba shi ne mutumin da ya dace ya jagoranci Najeriya a wannan lokaci da ake ciki.
Ojudu ya yi wannan furuci ne a yayin wata hira da jaridar The Sun ta bibiya a ranar Litinin 30 ga watan Disambar 2024.
Dan siyasar wanda ya taba yin aiki tare da Osinbajo, ya ce mai gidansa zai iya yin jagoranci mai inganci fiye da Shugaba Tinubu.
“Na yi aiki da Tinubu, kuma ina ganin cewa falsafarsa ta ‘Emi Lokan’ ba ta dace da wannan lokaci ba.”
“Da Osinbajo ya samu dama, Najeriya za ta kai mataki mai girma, amma hakan bai faru ba.” – Babafemi Ojudu