Sannu-sannu dai Faransa na ci gaba da rasa tasirin da take da shi a wannan yanki na Afirka ta Yamma, da irin wannan mataki da tsofaffin kasashen da ta yi wa mulkin mallaka ke kawo karshen yarjejeniyar zaman sojin Faransar a kasashen.
A wani jawabi na karshen shekara da Shugaba Alassane Ouattara ya gabatar ga kasar, ya ce matakin kuduri ne na neman zamanantar da dakarun kasar tasa.
Matakin ya kasance irin na Nijar da Mali da Burkina Faso, wadanda tuni suka raba gari da sojojin tsohuwar uwargijiyar tasu amma kuma bayan da sojoji suka yi juyin mulki a kasashen tare kuma da karuwar kyama da kin jinin Faransar da ake yi a kasashen.
Sai Chadi wadda babbar kawa ce ga kasashen yammacin duniya a kan yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi a yankin wadda ita ma ta kwatsam a watan Nuwamba ta sanar da aniyarta ta raba gari da Faransar a yarjejeniyar sojin.