Ruwan sama kamar da bakin kwarya yayi sanadiyar rufe makarantu da Asibiti a kasar Ghana

An Rufe Makarantu Sa Asibitoci A Ghana Sakamakon Mummunar Ambaliyar Ruwa
An Rufe Makarantu Sa Asibitoci A Ghana Sakamakon Mummunar Ambaliyar Ruwa
An rufe makarantu da asibitocin ne a yankin Tetegu da ke karamar hukumar Ga ta Kudu, inda hukumar ba da agajin gaggawa tare da rundunar soja ne suka dinga taimakawa jama’ar wannan garin.

Wannan shi ne karo na farko da irin wannan ambaliyar ta taba faruwa kamar yadda mutanen da abin ya shafa suka bayyana a lokacin da sSke kirga asarar da suka yi.

An Rufe Makarantu Sa Asibitoci A Ghana Sakamakon Mummunar Ambaliyar Ruwa
An Rufe Makarantu Sa Asibitoci A Ghana Sakamakon Mummunar Ambaliyar Ruwa
Yayin zantawa da daya daga cikin wadanda abin ya shafa ta ce “ni da ‘ya’ya na za mu tafi wurin ‘yar uwata da ke Kasoa domin neman agaji, kayan abincinmu, sutura, komai namu ambaliyar ta dauke ta tafi da su.”

Mallam Ibrahim Bossu Sarkin zangon Tetegu daya daga cikin anguwar da ambaliyar ruwar ya rusa da su, ya ce kowace shekara hukumar kula da madatsar ruwar ta kan sanar da su kafin bude kofofin madatsar ruwar Weija.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments