Burtaniya Da Faransa za su jagoranci ƙasashe 40 kan batun buɗe Mashigar Hormuz

Firaministan ƙasar United Kingdom, Keir Starmer, ya bayyana cewa Birtaniya tare da France za su karɓi baƙuncin wani babban taro da zai haɗa ƙasashe sama da 40 domin tattauna batun rufe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz da kuma hanyoyin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa na duniya.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Firaministan ya ce wannan matsala ta katsewar muhimmin hanyar sufuri na ƙara ta’azzara matsin tattalin arziki a duniya.

Starmer ya ƙara da cewa taron da ake shirin gudanarwa zai mayar da hankali ne kan samar da tsari na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe da dama domin kare zirga-zirgar jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments