Yan Najeriya sun yi barazanar yin bore muddin gwamnatin kasar ta gaza daukar matakin dakatar da babban bankin kasar CBN kan wa’adin da ya bayar na daina karba da kuma amfani da tsoffin takardar kudin da aka canja.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babban bankin Najeriya CBN ya ce ba gudu ba ja da baya game da wa’adin da ya sanya na daina amfani da wasu tsoffin takardun kudin ƙasar daga ranar 31 ga watan Janairu, duk kuwa da kiraye kirayen da bangarori da dama a cikin kasar su ka yi kan a tsawaita wa’adin.
Shugaban Kungiyar Matasan Arewa maso Gabas, Alhaji Abdulrahman Buba Kwacha, ya ce wannan mataki zai takurawa talaka tare da tura shi bongo kuma su baza su yadda da wannan abu ba.
‘Ƴan Najeriya da dama sun yi korafi game da karancin sabbin takardun kudin, inda suka ce har yanzu bai wadata ba kuma ya zuwa wannan lokaci bankunan kasar na bai wa kwastomominsu tsoffin takardun kudi.
A nasa bayanin, Mataimakin Shugaban Kungiyar Sauya Tattalin Arzikin Arewacin Najeriya, Abubakar Muhammad Kantato, ya ce wannan wa’adi da bankin CBN ya bayar ba karamin ruguza tattalin arzikin yanki arewacin Najeriya zai yi ba, la’akari da yan’kasuwa da ke kauyuka da babu bankuna da za su gudanar da hada hadar kasuwancinsu.
Gammayyar kungiyoyin arewacin Najeriya CNG ita ma ta bi sahu wajen kira da ‘yan kasar da su fito su nema wa kansu mafita kan wannan batu, kamar yadda shugabanta Nastura Ashir Shariff ya bayyana.
Tun da fari dai Bankin CBN ya bayyan cewa, sauya fasalin kudaden da aka yi zai yi tasiri matuka wajen taimaka wa kasar ta hanyar magance matsalar yaduwar kudi ba bisa kai’da ba da matsalar cin hanci da rashawa, kazalika sabbin kudaden za su inganta tatalin arzikin Najeriya da kara wa kudin kasar daraja. Lamarin da yan kasar ke gannin lokacin da aka diba don cimma hakan ya yi kadan.