Rahotanni na nuni da cewa yanzu taadda sun bude wuta a kauyen Damari yayin da ‘yan kungiyar Ansaru ke yi wa jama’ar yankin wa’azi inda suka kashe mutanen kauyen biyu.
Rahoton yace ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Damari da ke karkashin gundumar Kazage a Gabashin karamar hukumar a kokarinsu na fatattakar mayakan Ansaru daga kauyen.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka mamaye al’umomin Gabashin karamar hukumar, inda suke jagorantar mutanen kauyukan kan hare-haren ‘yan bindiga.
Ishaq Usman Kafai, shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an dauki tsawon sa’a guda ana arangama tsakanin kungiyoyin biyu.
A cewarsa, ‘yan kungiyar ta Ansaru wadanda su ma dauke da muggan makamai sun yi galaba a kan ‘yan bindigar wanda hakan ya sanya su (’yan bindiga) suka janye daga kauyen.