Ma’aikatan wutar lantarki na barazanar sake rufe cibiyar rarraba wuta ta kasa.

Ma’aikatan wutar lantarki na barazanfar sake rufe cibiyar rarraba wuta ta kasa.
Daga Walid Hari.

Akwai fargaba a kasar nan yayin da ma’aikatan wutar lantarki, karkashin inuwar kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa, NUEE, su ka sake yin barazanar rufe cibiyar rarraba wutar lantarki ta kasa.

A cewar ma’aikatan wutar lantarkin, wa’adin makwanni biyu da gwamnatin tarayya ta yi na sasanta wa kan rikicinsu ya wuce kuma ba a yi komai ba

Da ya ke zantawa da manema labarai a Kaduna a jiya Alhamis, Comrade Dukat Ayuba, sakataren kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma na NUEE, ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da tattaunawa, za a rufe cibiyar rarraba wutar lantarki ta kasa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments