An dakatar da tashin jiragen safe yayin da aka bar fasinjoji cikin damuwa sakamakon rufe filin sauka da tashin jiragen sama da Murtala Muhammad dake Legas da aka yi a safiyar Talata.
Jaridar TheCable ce, ta ruwaito hakan inda tace ma’aikatan filin jirgin suna zanga-zanga kan korar wasu mambobin Bi-Courtney Aviation Services Limited da aka yi ne.