Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin, ta ce kumbon dakin gwaji na Mengtian, ya yi nasarar hadewa da tashar binciken sararin samaniya ta kasar wato Tiangong
Mengtian, wanda shi ne dakin gwaji na biyu na tashar Tiangong, ya hade ne da bangaren gaba na Tianhe, wato babban bangaren tashar, da misalin karfe 4:27 na safiyar yau Talata agogon Beijing, daga nan ne kuma ya shiga da’ira kamar yadda aka tsara. Hadewar bangaroroin biyu ya dauki kimanin sa’o’i 13.
Daga baya, dakin gwaji na Mengtian zai sauya mazauninsa kamar yadda aka tsara. Kumbon dakin gwaji na Mengtian, da takwaransa na Wentian da babban bangare na Tianhe ne za su hade su bada siffar T ta tasahar binciken sararin samaniya ta kasar Sin.