Gwamnan jihar Jigawa, Ahmed Umar Namadi, ya sake rasa ɗaya daga cikin iyalansa a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2024
Yaron gwamnan mai suna Abdulwahab Umar Namadi ya rasu da yammacin ranar Alhamis sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi
Rasuwar tasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan mahaifiyar Gwamna Umar Namadinta riga mu gidan gaskiya
Mai girma gwamnan jihar Jigawa, Gwamna Mallam Umar Namadi, na sanar da rasuwar wani daga cikin iyalansa, ɗansa Abdulwahab Umar Namadi.”