Cikin shessheka, tana kuka tamkar rayuwarta za ta fita, da ƙyar Hauwa’u ta iya faɗa wa wakiliyar BBC sunanta.
Daga nan ta sake fashewa da kuka yayin da al’umma ke ƙoƙarin kwantar mata da hankali kan mummunan ibtila’in da ya afka mata da asubahin ranar Talata.
Wani harin jirgin yaƙi, da ake zargin na sojojin Najeriya ne ya hallaka mutum 10 da raunata wasu guda shida a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto, ta arewa maso yammacin Najeriya.
Cikin waɗanda suka mutu akwai mahaifi da mahaifiyar Hauwa’u da kuma ƙannenta huɗu.
Duk da cewa ya zuwa lokacin da aka yi jana’izar mutanen 10 da yammacin Laraba – kamar yadda wakiliyar BBC ta shaida – rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba, kuma babu wani jami’in soja da ya halarci jana’izar, wannan ba shi ne karon farko ko na biyu ko ma na uku da sojojin Najeriya ke kai harin ‘kuskure’ kan fararen hula ba.
Ɗaya daga cikin harin da sojojin suka kai na baya-bayan nan wanda har yanzu raunin da ya haifar a zukatan ƴan Najeriya bai warke ba, shi ne harin da jirgin soji maras matuƙi na rundunar sojin Najeriyar ya kai kan masu ibada a ƙuyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Hukumomi a jihar ta Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 85 harin da aka kai kan masu taron Maulidi, domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad a ranar 3 ga watan Disamban 2023.
Buhari – jihar Yobe a 15 ga watan Satumban 2021
Sai kuma harin da rundunar sojin saman Najeriya ta ce jirginta ya kai bisa kuskure kan ƙauyen Buhari da ke Yunusari a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya a watan Satumban 2021.
Shaidu sun ce harin jirgin saman ya kashe aƙalla mutum goma, baya ga gommai da suka jikkata, cikinsu har da mata da ƙananan yara.
A watan Janairun 2017 ma, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai hari a wani sansanin ƴan gudun hijirar rikicin Boko Haram da ke garin Rann – jihar Borno, a arewa maso gabashin ƙasar.