Kungiyar yarbawa ta Afenifere taci gaba da daga murya ga shugaba Buhari

Kungiyar Kare muradun yarbawa ta Afenifere ta bukaci shugaban kasa Muhammad Buhari ya yayi fashin baki a kan furucin da yayi wanda yace,  “clean up the mess in Nigeria into reality.

 

Sakataran kungiyar ta Afenifere na kasa mista, Jare Ajayi shine ya furta hakan inda yace kalaman na Buhari na nuni da cewa akwai lauje cikin nadi.

 

Buhari yayi furucin ne a lokacin da shugabannin gudanarwa na makarantar ICAN a Abuja.

 

A cewar kungiyar Afenifere duda gogewar da shugaba Buhari suke ganin yana da ita na kafin a zabe shi a wannan karo ya jagoranci al’umma a baya kuma yanzu ya kwashe shekaru bakwai amma kawo daideto ga yan Najeriya yafi karfin sa.

 

Kazalika ta Kara da cewa har yanzu akwai rikice-rikice da al’umma suke da bukatar a kawo karshen su a kasar nan da kuma matsalolin tsaro da suke ci gaba da addabar Al’ummar kasar wanda yakamata shugaban kasa Muhammad Buhari yayi aiki tukuru dan kawo karshen su.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments