Ibrahim sani gama
Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen malam Kato ta sha alwashin gudanar da ayyuka kafada da kafada da Sabon kwamishinan sufuri da gidaje na jihar kano Alhaji sale kausani domin bunkasa harkokin sufuri a jihar nan.
Shugaban matasan kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen malam Kato Alh samaila Gredy ne ya bayyana haka a lokacin da yake Karin haske ga manema labarai dangane da Sabon kwamishinan sufuri da gidaje da Gwamnatin kano ta nada, wanda ya gudana a ofishinsa dake tashar malam Kato.
Shugaban matasan kungiyar yace kungiyar ta shirya tsaf domin neman damar tattaunawa da kwamishinan kasancewar akwai kudirce kudirce da za su inganta harkokin sufuri dama zayyana masa matsalolin da gamayyar kungiyoyin sufuri suke fuskanta a wannan lokaci da muke ciki, inda yace, direbobi suna fuskantar kalubale ta Fannin sanaarsu daga bangarori da dama.
Yace, daga cikin kalubale da direbobi suke Fama da su, akwai rashin cikakken tsaro da rashin kyawawan hanyoyin da za su rika aiwatar da ayyukansu da cin zarafin direbobi da wasu daga cikin jamian tsaron hanya suke yiwa yankungiyar.
Samaila Gredy, ya shawarci kwamishinan sufuri da gidaje Alh sale kausani, da yayi amfani da wannan lokaci da yake ziyarce ziyarcen guraren dake karkashin Ma, aikatarsa domin ganin yadda alamura suke gudana, inda yake kira da ya rika ziyartar tashoshin motocin haya domin sanin halin da yake faruwa da kuma, ganewa idanunsa yadda alamura suke tafiya.
Shugaban matasan yace, rashin tattaunawa da kungiyoyinsu na direbobi Yana daya da ga cikin abubuwan da suke kawo koma baya da durkushewa harkokin sufuri, saboda, direbobi ne za su bayyana Maka halin da suke tsintar kansu a ciki, sabanin tuntubar wadanda ba Sana,arsu bace.
Haka zalika, yace kungiyar tana ragewa Gwamnati nauye nauye ta fannoni da dama, musamman ta hanyar samarwa matasa ayyukan yi da samar da kudaden haraji wanda sune ake gudanar da ayyuka na musamman Dana raya karkara da sauran abubuwan ci gaba.
Daga karshe yayi kira ga yankungiyar da su Kara baiwa Kungiyar cikakken hadin Kan daya dace domin ciyar da kungiyar gaba.