Jkadan kasar China dake jamhuriyar Nijer Jiang Feng, ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar, kana shugaban jam’iyyar MNSD Sani Oumarou, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin karo na 20.
A yayin ganawarsu, Jiang Feng ya bayyana cewa, kwanan baya, an cimma nasarar gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20, inda aka tabbatar da hanyar neman ci gaban kasar Sin a nan gaba
A gefe guda kuma kasar na kara habaka karfin hadin gwiwa a tsakanin ta da kasashen waje.
Sin tana son yin amfani da wannan dama wajen zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da Nijer a fannoni daban daban, da kuma karfafa mu’amala tsakanin jami’an hukumomin kafa dokoki, ta yadda za a inganta huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare kuma, Seini Oumarou ya taya Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin murnar cimma nasarar gudanar da taron, da kuma taya Xi Jinping murnar zama babban sakataren kwamitin kolin JKS. Ya ce, cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba bisa jagorancin JKS, lamarin da ya ba da tallafi ga al’ummomin kasar da yawansu ya kai biliyan 1.4. Kaza lika jamhuriyar Nijer tana mai da matukar hankali wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, tana kuma fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen kara mu’amalar hukumomin kafa dokoki a tsakanin kasashen biyu, domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu kamar yadda ake fata.