’Yan uwa da abokai, maza da mata, barka dai. Lokaci na gudu cikin sauri, kuma sabuwar shekara na gabatowa. Ina yi wa kowa gaisuwa da fatan alheri daga Beijing.
A shekara ta 2024, mun gudanar da ayyuka iri-iri cikin hadin-gwiwa, da cimma nasarori tare da haye wahalhalu, kuma akwai abubuwa da dama da suka burge mu, wadanda ba za mu iya mantawa da su ba a wannan shekarar dake karewa.
Mun nuna himma da kwazo wajen shawo kan tasirin da aka haifar sakamakon sauye-sauyen halin da ake ciki a gida da waje, da bullo da wasu jerin manufofi, da zummar samar da ci gaba mai inganci. Tattalin arzikin kasar Sin ya samu farfadowa, kuma bisa hasashen da aka yi, jimillar GDPn kasar zai zarce kudin Sin Yuan tiriliyan 130. Har wa yau, yawan hatsin da aka samar a duk fadin kasar ya wuce kilogiram biliyan 700, al’amarin da ya sa al’ummar kasar Sin suka kara samun abinci. Kaza lika, sassa daban-daban na kasar sun samu ci gaba cikin hadin-gwiwa, inda birane da garuruwa suka bunkasa bisa sabon salo, a yayin da yankunan karkarar kasar suka samu farfadowa. Haka kuma kasar ta zurfafa ayyukan ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, matakin da ya kara raya kyakkyawar kasar Sin.
Kasar Sin ta himmatu wajen raya sabon karfin samar da hajoji masu karko, kuma an samu bullar wasu sabbin sana’o’i da ayyuka da salo, inda a karo na farko yawan motoci dake aiki da sabbin makamashi da kasar ta kera ya zarce miliyan 10, har ma an samu sabbin nasarori a fannonin da suka shafi kirar sassan harhada kayan laturoni na IC, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI, da kuma fasahar sadarwar zamani da ake kira quantum communication. Haka kuma, a karo na farko na’urar bincike ta Chang’e 6 ta dauko samfura daga bangaren bayan duniyar wata, kana babban jirgin ruwan binciken teku na Mengxiang ya gudanar da bincike a sashen teku mai zurfi, kuma hanyar da ta ratsa teku mai hada biranen Shenzhen da Zhongshan, na taimakawa ga saukaka harkokin sufuri, kuma an kara raya tashar bincike ta Qinling dake yankin Antaktika, al’amuran da suka shaida babban buri, gami da kwazon Sinawa na raya harkokin da suka shafi sararin samaniya da teku.
A shekarar da muke ciki, na yi tattaki zuwa sassa daban-daban na kasar Sin, inda na ganewa idanuna yadda jama’a ke jin dadin rayuwa. Tufa nau’in Huaniu dake birnin Tianshui na da girma kuma da dadi, har ma ana kama kifaye masu yawa a kauyen Aojiao dake gundumar Dongshan. Kogon dutse na Maijishan ya bayyana dimbin tarihi na shekaru sama da dubu, yayin da iyalai dake zaune a titin Liuchi suna kiyaye nagartattun halaye na zuriya bayan zuriya. Mutane da dama suna ziyartar tsohon titin al’adu dake birnin Tianjin, kuma ’yan kabilu iri-iri na zaune cikin jituwa kamar ’yan uwan juna a unguwannin birnin Yinchuan. Na kuma maida hankali sosai kan wasu batutuwan da suka jawo hankalin jama’ar kasar, ciki har da neman guraban ayyukan yi, da kara samun kudin shiga, da harkokin da suka shafi tsoffi da yara, da batun samar da ilimi da kiwon lafiya da sauransu. A shekarar 2024, an kara kudin fansho mafi kankanta ga tsoffi, da rage kudin ruwan da bankuna suke karba daga masu karbar rancen sayen gidaje, da kara saukaka ayyukan ganin likita a sassa daban-daban, ta hanyar fadada wuraren da ake iya biyan kudin inshorar ganin likita kai-tsaye, tare kuma da bullo da manufar sayen sabbin hajoji ta maye gurbin tsoffin hajojin da ake da su, al’amarin da ya kara inganta rayuwar al’ummar kasar, wadanda suke kara nuna gamsuwa ga rayuwarsu.
A yayin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa, ’yan wasannin kasar Sin sun nuna himma da kwazo, inda suka cimma manyan nasarori da ba’a taba ganin irin su ba a tarihin halartar gasanni a kasashen waje da ’yan wasan kasar Sin suka je, al’amarin da ya shaida jajircewar matasan kasar. A wannan shekara kuma, rundunonin sojin ruwa, da na sama na kasar Sin sun yi bukukuwan murnar cika shekaru 75 da kafuwa, inda suka nuna kuzarinsu sosai. Domin shawo kan bala’o’i daga indallahi, kamar su ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa, mahukunta ’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin sun wuce gaba, da zama tsintsiya madaurinki daya don taimakawa juna. ’Yan kwadago, da masu gina kasa, da masu raya sana’o’i masu tarin yawa sun nuna hazaka wajen neman cimma burinkansu. Ni kuma na bayar da lambobin karramawa ga wadanda suka samu lambobin yabo na kasa da lambobin yabo na girmamawa na kasa, kuma sun cancanci yabon. Duk wani mutum dake nuna jajircewarsa wajen aiki shi ma ya cancanci yabo.
Duniya na fuskantar sauye-sauye da rikice-rikice a halin yanzu, kuma a matsayinta na babbar kasa dake daukar nauyi a wuyanta, Sin na himmatuwa wajen kawo sauye-sauye ga tsarin tafiyar da harkokin duniya, da zurfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Muna kokarin zurfafawa, gami da inganta ayyukan da suka shafi shawar