Wani jami’in Amurka ya tabbatar wa kafar yada labarai ta BBC cewa ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta sanar wa majalisar dokokin ƙasar shirinta na sayar wa Isra’ila makamai da suka kai na dala biliyan takwas.
Makaman – waɗanda dole sai majalisar dattawa da ta wakilai sun amince a sayar da su – sun ƙunshi makamai masu linzami da bama-bamai da sauran nau’ikan harsasai.
Matakin na zuwa ne ‘yan kwanaki kaɗan kafin Joe Biden ya sauka daga muƙamin shugabancin ƙasar.
Amurka ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi mata na dakatar da bai wa Isra’ila goyon bayan soji sakamakon kashe fararen hula masu yawa a yaƙin Gaza.
A watan Agustan shekarar da ta gabata ma Amurka ta amince da sayar wa Isra’ila makaman yaƙi da suka ƙunshi jiragen yaƙi da sauran kayan aiki na kusan dala biliyan 20.