Jami’ai sun ce ƴanbindiga sun kashe sojojin Kamaru aƙalla shida a wani hari da suka kai kan iyakar ƙasashen biyu.
Wani ɗan majalisa a yankin Akwaya da ke kudu maso yammacin Kamaru ya ce ɗaruruwan makiyaya ne suka kai hari kan wani sansanin soji.
Wani basarake a yankin ya ce maharan sun ƙona gidansa.
Ɗan majalisar yankin ya ce harin ramuwar gayya ne bayan sojojin Kamaru sun kashe makiyaya da dama kwana guda kafin harin.