An bai wa dan wasa jan kati a dakika tara a French League
Filin wasannin Aksam Radio tare da Walid Y Hari.
Mai tsaron baya, Jean-Clair Todibo ya karbi jan kati a kankanin lokaci da fara wasa a tarihin Ligue 1.
An kori dan kwallon a dakika tara da fara wasan da Nice ta yi rashin nasara a gida da ci 1-0 a hannun Angers ranar Lahadi.
An bai wa tsohon dan wasan Barcelona jan kati, sakamakon wata keta da ya yi, nan da nan alkalin wasa ya sallameshi daga karawar.
Tsohon dan wasan Tottenham, Nabil Bentaleb shi ne ya ci wa Angers kwallon tun kan hutun rabin lokaci.
Ita kanta Angers ta karasa gumurzun da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa tsohon dan kwallon Southampton, Sofiane Boufal jan kati.
Dan kasar Ingila, Ross Barkley ya buga wa mai masaukin baki wasan, sai dai dan kwallon tawagar Wales, Aaron Ramsey na jinya.