Jama’a barkan mu da sake kasancewa a dai dai wannan lokaci ta cikin shirin Cuta da magani tare da ni Hasana B Sanusi.
A yau zamu kawo muku wasu daga cikin illolin shan ruwan sanyi, wanda muke fatan hakan zai taimaka wajan kauracewa amfani da shi a kowanna yanayi
1 TSAIDA BUGUN ZUCIYA:- bugun zuciya shike gyara dumin jiki da daidaita numfashi to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin yan film na kasar indiya da yan ball da boxing da wrestling tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aikine yake jawo musu..
2 . LALATA TSARIN KAYAN CIKI:- shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan jawo matsalar hanji ulcer kenan ko kuma tashin zuciya. Yawancin masu shan ruwan sanyi suna yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar ciki
3. DAUKE KARFIN JIKI:- Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon cewa yayinda ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai naurorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin hakan yanasa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazxabi a hankali kuma sai kuji ya daina.?
4. CIWON MAKOGWARO DA DAKUSHEWAR MURYA:- Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har sukai ga basa amfaninsu mai kyau a mai sha yakai shekaru arbain sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ko muryar ta fashe kwatankwacin mashayin taba