Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sha al’washin Samar da sabbin dokokin da za su hukunta masu yin bara da kananan yara ko yan jagora, kuma a kan titunan kwaryar birnin Kano.
Mataimakin Babban kwamadan hukumar, aiyuka na musanman malam Hussain Ahmad Cediyar kuda shine ya sanar da hakan a ya yin hulin mabarata 39 wadan da Dakarun hukumar Hisbah su ka kama na aiwatar da laifin yin bara, ciki har da masu dauke da kananan yara a manyan titin Kano.
Malam Hussain Ahmad Cediyar Kuda ya kara da cewar Hisbah ba zatayi kasa a gwaiwa ba, wajen Samar da sabbin hanyoyin kawar da masu yin bara dukkanin ma su yi musu jagora, mutukara, a kan titunan kwaryar birnin Kano ko a shataletalen da sauran wuraren ba da hunnun motoci masu kai komo.
Tun da fari jami’in hukumar Hisbah mai kula hana bara a kan titunan kwaryar birnin Kano, malam Abubakar Salihu yace sun sami nasar kamo mabarata a kan titi maza da mata 39 ciki har da yan jagora ya yin da su me tsaka da yin bara a kan titunan, Dan Agundi da titin murtala Muhammad way da titin gidan murtala da titin zuwa gidan gwamna da danjar magwan
Malam Abubakar salihu ya ga ba da cewar sauran wuraren sun hadar da kofar famfo da kofar kabuga da shataletalen Tal’udu da titin gidan shatima duk a kwaryar birnin Kano.