Shugaban Hukumar KAROTA na jihar kano
Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi
Ya Gwangwanje wani jami’in Hukumar Karota mai Suna Halilu Kawu Jalo da kyautar Naira Million daya, biyo bayan Cin Hancin Naira 500,000 da wasu masu motar giya suka bashi yaki karba a Safiya yau Alhamis
28-072022. Cin Hancin da suka bashi yaki karba yabiyo Bayan kama motocin giya guda 2 da Jamin Karotar yayi Wanda kimar kudin giyar ya Haura Sama da Naira Million 50.
Daga wakilin aksammedia B.imam
da yake jawabi Shugaban Hukumar KAROTA yace yana daukar irin Wannan matakin ne dan karawa duk wani jami’i daya kaucewa karbar Rashawa dan kara masa karfin guiwa a yayin gudanar da aikinsa.
Idan Buku manataba Shugaban Hukumar ta karota yataba daukar irin Wannan matakin akan wani jami’in dan Sanda dake aiki a Hukumar kare Hakkin mai siya da mai siyarwa ta Jihar kano wato (Consumer) a wancen lokacin.