- Kungiyar wayar da Kai da tallafawa masu larurar cutar amosanin jini ta jihar Kano ta tallafawa da kuma wayar da kan matasa akan cutar a fadin kasarnan.
Shugaban kungiyar Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu ne ya bayyana hakan a lokacin da kungiyar ta Kai wata ziyara domin wayar da kan dalibai mata a makarantar kawaji da makarantar yammata ta Jogana dake nan kano.
Maharazu Ibrahim yace kuginyar a shirye take wajen ganin ta ta cigaba da wayar da kan matasa dangane da illar cutar amosanin jini a rayuwar maaurata da irin wahalhalun da suke tsintar kan su a ciki a cikin muamalar auratayya.
Shugaban ya shawarci yan mata kan su rika yin gwajin jini da sauran gwaje gwaje domin kaucewa kamuwa da cututtuka wadanda daga bisani Zasu iya samun kansu acikin damuwa tsakanin su da yaran da suka haifa.
Daga wakilin aksammedia ibrahim sani gama
Maharazu ya kuma bayyana cewar an kafa wannan kungiyar domin tallafawa da wayar da kan alumma musamman matasa maza da mata wadanda basu yi aure ba, kan su rika gudanar da gwaje gwajen cututtuka a asibiti kafin su fara tattaaunawa akan yin aure duba da halin da alumma suka tsinci kansu bayan sun fara hayayyafa.
A jawabansu daban daban shugaannin makarantun da kungiyar ta Kai wa ziyara sun nuna matukar farin cikinsu bisa ziyarar da aka Kai musu domin wayar da kan dalibai mata Matsalar dake akwai akan illar cutar amosanin jini a cikin rayuwar maaurata.
Kazalika sun bayyana cewar dukkannin makarantun biyu Zasu cigaba da baiwa yammata shawarwarin da suka kamata musamman wadanda suke daf da kammala karatun sakandire, inda suka ce wasu da dama idan sun kammala karatu aure Zasu yi .
Taron Ya samu halartar likitoci da dama da suka yi bayani kan illoli da kuma kare kai daga kamuwa daga cutar Wanda ya gudana a jihar nan.