Tarayyar Turai (EU) na shirin kakaba takunkumi ga kamfanonin Amurka idan har Amurka ba ta janye ikirarin ta kan Greenland ba.
A cikin wadannan tsare-tsare, EU na iya takaita ayyukan manyan kamfanonin fasaha na Amurka a yankinta, ciki har da Google, X, da Microsoft. Bugu da ƙari, bankunan Amurka da kamfanonin hada-hadar kuɗi ma na iya fuskantar irin waɗannan takunkumai.
Majiyoyi daga cikin EU sun ce matakin na zuwa ne a matsayin martani ga abin da ƙungiyar ke kallon tsoma baki ko barazana ga ikon yankin Greenland, wanda ke da alaƙa da Denmark, mamba a Tarayyar Turai.
Har ila yau, jami’an EU sun bayyana cewa idan ba a samu maslaha ta diflomasiyya ba, to za su ɗauki ƙarin matakai masu tsauri domin kare muradun siyasa da tattalin arziƙin ƙasashen ƙungiyar a matakin ƙasa da ƙasa.









