2027, China Za Ta Gabatar Da Jirgin Fasinja Mai Gudun Hypersonic

China na ƙara bunƙasa fasahar jiragen sama, bayan da ta bayyana shirin ƙera jirgin fasinja mai gudun hypersonic wanda ake sa ran zai iya zagaya duniya baki ɗaya cikin awanni bakwai kacal.

Kamfanin Lingkong Tianxing Technology da ke birnin Beijing ya gwada samfurin jirginsa mai suna Yunxing, ya tashi a gudun Mach 4  inda ya ci mil 3,000 a cikin sa’a ɗaya abin da ke nuna babban mataki a hanyar fara jigilar fasinjoji ta jiragen hypersonic na kasuwanci. Kamfanin na fatan fara ƙera jirgin domin kasuwanci nan da shekarar 2027.

Abin da ya fi ba da mamaki shi ne abin da ke gaba. Injiniyoyi sun bayyana cewa haɗa jirgin da injin oblique-detonation mai amfani da man kerosene, wanda aka ƙera tare da Cibiyar Injiniyan Ƙarfin Injin ta Beijing, na iya kaiwa jirgin gudun Mach 16 a nan gaba.

Idan aka cimma wannan fasaha, ba wai kawai za ta sa tafiye-tafiye su zama masu sauri ba, har ma za ta sauya yadda duniya ke hulɗa a fannin tafiye-tafiye, kasuwanci da motsin ɗan Adam gaba ɗaya. Duk da cewa har yanzu akwai manyan ƙalubalen fasaha da tsaro, ci gaban da China ke samu na nuna cewa jiragen fasinja masu saurin hypersonic ba labarin almara ba ne gasa ce da ta riga ta fara.

A nan gaba kusa, duniya na iya zama ƙanana fiye da yadda ake zato.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments