Hukumomin Najeriya sun sanar da janye dokokin corona ga masu shiga kasar ta jiragen sama.
Sanarwar ta ce hukumomi za su daina tambayar shaidar yin rigakafin corona ko akasin haka ga duk fasinjan da ya sauka kasar ta jirgin sama. Sai dai mahukuntan na Najeriya sun shawarci fasinjojin da suka haura shekaru 60 ko kuma ke da wata rashin lafiya ta dabam da su rika sanya takunkumin kariya.
Adadin Kimanin mutum 266,000 ne dai Najeriya ta ayyana sun kamu da annobar corona tun da ta bulla a kasar a shekara ta 2020. A cikin wannan adadi hukumomi sun ce mutum kimanin 3,000 cutar ta yi ajalin mutuwarsu a Najeriya.