Daraktocin biyu na yakin neman zaben Tinubu sun zargi jaridar ta Thisday da cin zarafi da tursasa wa dan takarar shugabancin Najeriya a APC, Bola Tinubu, don ya halarci taron sauraro manufofin ‘yan takarar shugabancin kasar, duk da bayanin da kwamitin yada labaran takararsa ya yi cewar dan takarar tasu ba zai samu zuwa taron ba, bisa la’akari da yadda kafafen yada labaran ke amfani da kalaman da ba su dace ba a kansa.
“Dukkan kwamitin yakin neman zaben dan takararmu na da ‘yanci su zabi tsare-tsaren da za su yi amfani da su wajen isar da sakonsu ko su yi magana kai-tsaye da ‘yan Najeirya”.
Haka kuma sun nanata cewar ba za su taba yarda da zagon kasa, ko barazana da cin zarafin daga jaridar Thisday.
“Dan takararmu ba zai yarda wasu su bata masa suna ba, da dauke masa hankali daga abin da ke gabansa, don sun ga shi ne a kan gaba a cikin masu neman shugabancin Najeriya, shi ya sa suka fito da irin wannan yarfen na siyasa,” in ji kwamitin yakin neman zaben Tinubu.