Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arzikin Kasar, Kwankwaso
 Sanata Rabiu Kwakwaso ya fara bayyana abubuwan da zai yi idan ya zama shugaban kasar Najeriya Hukumar zabe ta INEC ta bude filin fara yakin neman zabe tun ranar Larabar da ta gabata Rabiu Musa
Kwankwaso dai shine Éan takarar da Jam’iyyar NNPP ta tsayar a Shugaban Ĉasa
Ĉan takarar shugaban kasa na jamâiyyar NNPP, Sanata Rabiâu Kwankwaso, a ranar Litinin din nan data gabata, ya yi alkawarin habaka tattalin arzikin kasar tare da sake fasalin Nijeriya idan aka mara masa baya a zaben shekarar 2023
Kwankwason ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Jalingo Babban birnin Jihar Taraba, ya kuma yi alkawarin sanya ilimi a matsayin farko a gwamnatinsa, rahoton Punch.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya kara da cewa gwamnatinsa za ta samar da yanayi mai kyau ga kananan âyan kasuwa ta hanyar bunkasa yanayin kasuwancinsu tare da karfafawa mata da matasa gwuiwa dan damawa dasu aharkokin kasuwanci.
Ya kara da cewa, âZa mu ba da fifiko kan ilimi, zamu magance matsalar rashin tsaro da yanayi mai kyau dan haÉaka kasuwanciâ
Da wadannan matakan zamu samawar da Ĉ´an kasa damarmaki haÉi da bude musu hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu.
âZa mu inganta abubuwan da ake samarwa a gida da kuma tsarin shigo da kayayyaki da samar da ayyukan yi A cikin gida. Wadannan da ma wasu da dama su ne batutuwan da zamu maida hanakali a kai.
âKullum muna tashi mu ga Ĉudin kasar nan darajarar sa tayi Ĉasa, kullum Ĉudin kasashen waje kara hawa yak e. wannan na cikin abun da gwanati ta kamata ta kalla; amma ina, ku duba kuga yadda kullum tattalin arziki ke tabarbarewaâ