• About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
No Result
View All Result
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
Home HAUSA NEWS

China ta magantu akan taron Amurka da kasashen Africa

Aksam Media by Aksam Media
December 14, 2022
in HAUSA NEWS
0
0
SHARES
Share on FacebookShare on Twitter

Jakadan kasar Sin a Amurka Qin Gang, ya karyata zargin cewa wai Sin na danawa kasashen nahiyar Afirka tarkon bashi, inda ya ce kamata ya yi nahiyar Afirka ta zama wurin hadin gwiwar kasa da kasa, maimakon daukar ta a matsayin wani fage na gwabza takara, domin cimma burikan kasashen da suka ci gaba.

Tsokacin jakada Qin Gang, ya zo ne a jajiberin taron bunkasa dangantakar Amurka da kasashen Afirka, wanda shugaba Joe Biden zai jagoranta a birnin Washington.

RelatedPosts

Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya

Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya

April 1, 2023
Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu

Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu

April 1, 2023

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

March 31, 2023

Yayin kwarya-kwaryar tattaunawa da kafar watsa labarai ta Semafor dake Amurka a jiya Talata, gabanin bude taron na Washington, Qin ya ce “Ko kadan jarin da Sin ke zubawa a Afirka, da ma tallafin kudade da kasar ke baiwa nahiyar ba tarkon bashi ba ne”.

Jakadan na Sin ya yi fashin baki, game da sakamakon wani bincike da cibiyar “Debt Justice” dake Birtaniya ta wallafa a watan Yuli, inda ya ce adadin bashin da hukumomin kudi masu zaman kansu na kasashen yammacin duniya ke bin kasashen Afirka, ya ninka wanda Sin ke bin kasashen nahiyar har sau 3, kuma yawan kudin ruwa da hukumomin kudin na yammacin duniya ke cazar kasashen Afirka ya ninka na kasar Sin.

Bugu da kari, jakada Qin ya tabo batun dage wa’adin biyan bashi da kasashen G20 suka gabatar, inda ya ce Sin na kan gaba wajen aiwatar da wannan manufa, inda ta zamo ta farko wajen dage wa’adin biyan bashin da take bin kasashe daban daban, cikin daukacin kasashe mambobin kungiyar ta G20.

Game da taron na Amurka da kasashen Afirka, jakadan ya ce yana fatan Amurka za ta fito da kwararan matakai da za su ingiza ci gaba da wadatar nahiyar Afirka. Kaza lika ya yi kira ga Amurka da ta yi hadin gwiwa da Sin, ta yadda a matsayin su na kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, kuma mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD, za su iya hada karfi da karfe wajen bunkasa zaman lafiya, da tsaro da bunkasar nahiyar Afirka.

Har ila yau, ya kamata su sauke nauyin dake wuyansu, kasancewarsu manyan kasashe da ya dace su cika alkawuran da suka dauka a matakin kasa da kasa.

Taron birnin Washington na bunkasa hadin gwiwar Amurka da kasashen Afirka, zai gudana ne tsakanin ranakun Talata zuwa Alhamis, ya kuma hallara shugabanni daga kasashen Afirka 49, da kuma sassa daban daban na masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci da cinikayya.

ShareTweetSendSharePin
Previous Post

from the kano Emirate Council during the emir of kano visit to algeria

Next Post

Idan gwamnati ta inganta makarantun kimiyya da fasaha Dalibai zasu daina jiran ta basu aikin office: Dr Wada Sale

Aksam Media

Aksam Media

RelatedPosts

Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya
HAUSA NEWS

Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya

by Aksam Media
April 1, 2023
0

Fitaccen mawakin nan da ke sharafi a wannan zamani, Hamisu Breaker ya musanta zargin da ake yi na cewa shi...

Read more
Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu

Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu

April 1, 2023
Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

March 31, 2023
INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

March 31, 2023
Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

March 30, 2023
Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake

Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake

March 30, 2023
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Login
Notify of
guest
guest
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments
  • Trending
  • Comments
  • Latest
Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

March 10, 2023
Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

March 29, 2023
Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

February 21, 2023
INEC tayi umarnin kara gudanar da zabe a jihar Kogi

Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

March 19, 2023
CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

2
Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

1
Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

1
Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

1
Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya

Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya

April 1, 2023
Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu

Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu

April 1, 2023
Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

March 31, 2023
INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

March 31, 2023
  • Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya
HAUSA NEWS

Dalilin da yasa Breaker yace Babu wata alaƙar soyayya tsakanin sa da Rukayya

Fitaccen mawakin nan da ke sharafi a wannan zamani, Hamisu Breaker ya musanta zargin da ake yi na cewa shi ...

April 1, 2023
Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu
HAUSA NEWS

Bayan karbar kaddamar faduwa da Gawuna yayi APC ta garzaya kotu

Babbar Jam’iyar adawa a Kano APC ta bayyana shirin ta na zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben da hukumar zabe ...

April 1, 2023
Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi
HAUSA NEWS

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

Daga khadija Abdullahi Aliyu Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya daga Darajar wasu Hakimansa da kuma nada ...

March 31, 2023
INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna
HAUSA NEWS

INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

Hukumar Zabe Mai Zaman Katta Ta Kasa INEC, yau tabawa zabban Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Malam Uba Sani shedar sakamako yin ...

March 31, 2023
Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri
HAUSA NEWS

Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

An kama wani ɗan jaridan Amurka da ke aiki da jaridar Wall Street Journal a Rasha inda aka zarge shi ...

March 30, 2023

Recent Comments

  • Ibrahim S kabara on Hukumar kula da ayyukan yan sanda ta raba lambobin kiran waya Dan sa Ido a ayyukan yan sanda a lokacin zabe
  • Abbas Jibril on Katu ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa ta hanyar Rataya
  • Walid Y Haris on Akwai Malaman cocin dake kallan batsa a yanar gizo ta wayoyinsu-Fafaroma
  • Abba Garba Sufi on Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.
  • Sani saadu aliyu on CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

wpDiscuz