Idan gwamnati ta inganta makarantun kimiyya da fasaha Dalibai zasu daina jiran ta basu aikin office: Dr Wada Sale

An bukaci gwamnatin tarayya ta Mai da hankali ga makarantun kimiyya da fasaha, duba da irin rawar da suke takawa wajen Raba matasa da Zaman kashe wando da matasan keyi a unguwanni.

Bukatar hakan ta fito ne ta bakin shugaban makarantar kimiyya da fasaha dake Kazaure wato Hussain Adamu federal polytechnic Kazaure, Dr wada sale a ganawar sa da manema labarai a ofishinsa.

Sale yace makarantun kimiyya na Kokarin kauda hankulan dalibai akan lallai Sai sun yi aikin gwamnati Wanda ya zuwa yanxu gwamnatoci ba su da guraben da zasu Iya daukar kowa saboda yawan da aluma suka yi da Kuma halin da tattalin arzikin kasa ya shiga.

A cewar sa Hakan yasa makarantun suka bujuro da wasu hanyoyin koyawa daliban sanaoi iri daban daban Dan su dogara da kansu ba Sai sun jirayi gwamnati ba.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments