Mataimakiyar shugaban kotun kolin kasar China, He Rong, ta ce sassan hukumomin shari’ar kasar Sin za su kara a zama wajan karfafa kariya musamman ta ikon mallakar fasahar IPR.
Rong tace hakan wani mataki ne na tallafawa kasar Sin wajen cimma dogaro da kai, da karfafa ilmomin kimiyya da fasaha.
Mai shari’ar ta bayyana hakan ne a yau Larabar 19-10-2022, a yayin taron manema labarai da ya gudana a gefen babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) karo na 20.
Ta kara da cewa za a samar da dokoki masu karfi na kare ikon mallakar fasahohi, musamman a fannonin da suka jibanci fasahar killace manyan bayanai, da na kwaikwayon tunanin bil adama, da kimiyyar binciken kwayoyin halittun bil adama.
Kaza lika kasar ta Sin zata kyautata aiwatar da matakan shari’a domin dakile babakere da takara maras adalci.