Babban bankin Nijeriya, ya kara kudin ruwa zuwa kaso 16.5, daga kaso 15.5, yana mai cewa, yunkurin na da nufin rage fadawa cikin tsanantar hauhawar farashin kayayyaki.
Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, ya shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, bayan taron yini biyu da kwamitin tsara manufofin kudi na kasar ya gudanar, an zabi kara kudin ruwan, amma bisa matsakaicin mataki, domin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki.
A cewarsa, kwamitin ya dauki matakin ne bisa la’akari da cewa, har yanzu ana fama da abubuwan da suka yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin, kamar rikicin Rasha da Ukraine da kuma tsaikon da aka samu a tsarin samar da kayayyaki.
Ya kara da cewa, kwamitin na ganin cewa, yayin da bukukuwan karshen shekara ke karatowa da kuma babban zaben kasar a farkon badi, za a samu yawaitar kashe-kashen kudi, lamarin dake barazana ga ci gaban da aka samu daga kara kudin ruwan da aka yi a baya.
Matakin na jiya dai, shi ne irinsa na 3 cikin watanni 4 da suka gabata.