An sake arangama tsakanin ‘ya’yan kungiyar Ansaru da kuma ‘yan-bindiga a yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari sakamakon da aka kashe ‘yan bindiga biyar.
KADUNA, NIGERIA – Dama dai yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari na fama da hare-haren ‘yan-bindiga na tsawon lokaci sai dai wasu al’ummar garin sun ce duk lokacin da ‘yan kungiyar Ansaru su ka je garin ‘yan-bindigan ba sa samun damar satar mutane da dukiyarsu.
Wasu mazauna garin Damarin sun shaidawa Muryar Amurka cewa, a daren Litinin din makon nan ma sai da ‘yan kungiyar Ansarun su ka kashe ‘yan-bindiga biyar.
Mutanen wadanda su ka nemi a sakaya sunan su bisa dalilan tsaro, sun ce suna fama da hare-haren ‘yan-bindiga a yankin sosai sai dai idan ‘yan kungiyar Ansaru sun shigo garin su kan basu kariya.
Wasu ‘yan bindiga da aka kama
Wasu ‘yan bindiga da aka kama
Masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya dai na garin cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa game da karbuwar ‘yan kungiyar Ansaru a gurin al’ummomin yankunan Birnin Gwari don gudun abun da ka iya biyo baya.
Ya ce matukar dai gwamnati ba ta gaggauta daukar matakan magance matsalar tsaro a yankin ba al’ummomi za su ci gaba da daukaka ‘yan kungiyar ta Ansaru tunda su ke kare su.
Labarin bayyanar ‘yan kungiyar Ansaru a wasu yankunan Jihar Kaduna dai ya dade sai dai Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce gwamnati na aiki tukuru kan maganar matsalar tsaro a Jihar baki daya.