Hukumar JAMB ta Fitar da wasu sauye-sauye da ta gudanar a kan jarabawar

Hukumar JAMB ta sanar da ɗan sauyi a lokacin isowar ɗaliban da za su rubuta jarabawar 2026 ta Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME), musamman waɗanda aka tsara su fara a zangon farko.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Litinin, hukumar ta bayyana cewa yanzu ana sa ran ɗaliban zangon farko su isa cibiyoyin jarrabawarsu da ƙarfe 7:00 na safe, maimakon 6:30 na safe da aka tsara a baya.

JAMB ta ƙara da cewa za a fara jarabawar da ƙarfe 8:30 na safe kuma za ta ƙare da ƙarfe 10:30 na safe.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ba a buƙatar ɗalibai su sake buga takardun shaidar jarabawarsu (exam slips) sakamakon wannan sauyi.

A jadawalin cikakken ranar da JAMB ta fitar, akwai zanguna huɗu na jarabawa da za su gudana daga ranar Litinin zuwa Juma’a, tare da sabbin lokuta da aka daidaita a dukkan rukuni domin tabbatar da gudanar da aiki cikin sauƙi a cibiyoyin Computer-Based Test (CBT) a faɗin ƙasar.

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments