Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ya bi doka da ƙa’ida wajen sauya fasalin takardun kuɗin ƙasar uku da yake shirin yi.
Kakakin CBN, Mista Osita Nwanisobi, namayar da martani ne ga Ministar Kuɗi Zainaba Shamsuna Ahmed, wadda ta ce ba a tuntuɓi ma’aikatarta ba kafin aiwatar da sauyin.
Da take magana lokacin da ta bayyana a gaban wani kwamatin Majasliar Dattawa ranar Juma’a, Zainab ta soki shirin tana mai cewa “ba lokacin da ya dace ba ne”.
Sai dai Mista Nwanisobi ya ce hukumomin CBN sun bi ƙa’ida wajen neman amincewar Shugaba Buhari kamar yadda sashe na 2(b) da sashe na 18(a) da sashe na 19(a) (b) na dokar CBN ta 2007 suka tanada don neman sauya fasali da samarwa da fara aiki da kuma yaɗa sabbin takardun kuɗi na N200 da N500 da 1,000.
A ranar Laraba ne babban bankin ya ba da sanarwar sake takardun na naira, inda ya ce kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasar na hannun mutane maimakon bankunan kasuwanci.
CBN ya bai wa ‘yan ƙasar wa’adin kwana 42 da su mayar da kuɗaɗen cikin bakunan kasuwanci kuma yana sa ran nan da 15 ga watan Disamba mai zuwa zai fitar da sabbin takardun N200 da N500 da N1,000.