Hukumomi a Ukraine sun gargaɗi mutane a birnin Kyiv da su kasance cikin shirin zama a duhu na sama da huɗu sakamakon ƙaruwar hare-hare da Rasha ke kaiwa.
Rashin wuta na damun biranen da ke tsakiyar Ukraine, ciki har da Dnipro.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce mutum kusan miliyan huɗu ƙarancin lantarkin ya shafa “amma luguden wuta ba zai karya lagonmu ba”.
A watan nan Rasha ta kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙi da Iran ke ƙerawa.
Hare-hare kan ƙare a kan tashoshin lantarki da sauran ababen more rayuwa. Mista Zelensky ya ce an lalata kusan ɗaya cikin uku na tashoshin lantarkin ƙasar.