Sashen tattalin arziki da zamantakewa na Majalisar Dinkin duniya ya fitar da wani sabon rahoto dake nuna cewa yawan mutane a Najeriya ya kai kimanin miliyan 216 a wannan shekara ta 2022, hakan ya bawa Najeriya damar cimma kaso 2.7 na al’ummar duniya.
Hukumar kididdigar yawan jama’a ta kasa da ke shirin kidaya a watan African shekara mai zuwa ta tabbatar da ingancin rahoton na Majalisar Dinkin Duniya.
Hakan na nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashe takwas da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Masar, Habasha, Indiya, Pakistan, Philipines da Tanzaniya dake bada gudumawa wajen saurin karuwar yawan mutane a duniya.