Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya roki mazauna jihar su yafe masa duk wani kuskure da ya yi a zamanin mulkinsa na tsawon zango biyu dake gab da karewa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito. Gwamna Masari ya nemi wannan afuwar ne a wurin taron ƙaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen jam’iyyar APC a jihar yau Litinin 31 ga watan Oktoba, 2022.
Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wurin kira ga mambobin APC, waɗanda ke ganin an musu ba dai-dai ba da su yafe musu, inda ya ƙara da cewa sun yafe wa kowa. Haka zalika, gwamnan ya maida martani ga wasu mutane da yake ganin sun yi wa jam’iyya All Progressive Congress da gwamnatinsa butulci sakamakon rashin cika buriknasu 100%.