Rundunar Yan sanda a jihar Anambra sun kai farmaki a wata maboyar ‘yan ta’adda a kauyen Nimo da ke karamar hukumar Njikoka
A Yayin farmakin, an kwace bama-bamai da dama tare da lalata gine-ginen da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen buya
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yaba da hadin kan da ake samu tsakanin hukumomin da jama’a wajen tabbatar da tsaro
Kakakin ‘yan sanda, na jihar SP Tochukwu Ikenga ne ya wallafa labarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 25 ga Disamba, 2024 a shafin Facebook.