Masarautar Burtaniya ta bayyana tsawon lokacin makokin Sarauniya.
Daga Walid Y Hari
Fadar Buckingham ta bayyana tsawon lokacin da za ta dauka tana makokin rasuwar Sarauniya, inda lokacin zai fara daga yanzu zuwa kwana bakwai bayan jana’izar Saruniyar.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ranar jana’izar Sarauniyar ba.
A sanarwar da ta fitar, fadar ta ce ”Bayan rasuwar mai martaba Sarauniya, mai martaba Sarki na son sanar da al’umar Burtaniya cewa fada za ta fara makoki ne daga yanzu, har zuwa kwana bakwai bayan jana’izar Sarauniya”.
Baya ga makokin kasa da ake sa ran firaminista za ta sanar yau, makokin fada shi ne makokin da iyalan gidan Sarauta, da ma’aikatan fadar, da wakilan fadar a wurare da kasashe daban-daban, tare da sojoji da da jami’an tsaron da ke aiki a fada.
Mutane da dama a fadin duniya na ci gaba da bayyana jimamin rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta hanyar ajiye furanni tare mika sakonnin jaje a ofisoshin jakadancin Burtaniya.