Iran ta ce Amurka da Isra’ila za su fice daga yankin ba tare da wata nasara ba

Shugaban rundunar Quds ta IRGC, Birgediya Janar Esmaeil Qaani, ya bayyana cewa Amurka da kuma gwamnatin sahyoniyawa za su tilasta ficewa daga yankin Gabas ta Tsakiya ba tare da sun cimma wata nasara ba.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Qaani ya ce hadadden gaban ‘yan gwagwarmayar “resistance” na da ƙarfi kuma yana da tasiri a duk faɗin yankin, yana mai cewa suna jiran abokan gaba na bil’adama. Ya ƙara da cewa ya kamata Amurka da Isra’ila su tuna yadda suka gudu hannu wofi daga Yemen, yankin Bab-el-Mandeb da kuma Tekun Bahar Maliya. “Yanzu ma za su fice daga yankin ba tare da wata nasara ba,” in ji shi.

Wannan furuci na Qaani ya zo ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa rundunar ruwan Amurka za ta fara killace mashigar ruwa ta Hormuz tare da tsayar da duk wani jirgin ruwa da ya biya haraji ga Iran a cikin ruwan ƙasa da ƙasa.

Sai dai rundunar CENTCOM ta Amurka ta ce wannan mataki zai shafi jiragen ruwa ne kawai da ke zuwa ko dawowa daga tashoshin jiragen ruwa na Iran. Ta kuma tabbatar da cewa sauran jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa da ba su da alaƙa da Iran za su ci gaba da samun ‘yancin zirga-zirga a mashigar.

Sojojin Amurka sun kuma sanar da cewa za su fara killace tashoshin jiragen ruwa na Iran daga ranar Litinin da misalin ƙarfe 14:00 na agogon GMT.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments