Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Hukumar Hisbah ta Kano ta magantu akan maganganun da wata mai suna Fatima Baffa Usman ta yada akan yanar gizo, inda tace mai gadin makabartar Dandolo ya hana yan uwan Wasu mata matattu binne gawar a makabartar.
Hukumar Hisbah ta nuna matukar damuwarta akan wanna maganganun domin ta samu korafe-korafe daga mabambantan mutane musamman mata wadanda suka kalubalanci maganar.
A bisa haka Hukumar Hisbah ta gayyaci matar domin tattaunawa, a inda ta fahimci kuskurenta ta kuma karrba, kana ta janye, tare da bada hakuri ga al ummar musulmi baki daya musamman matan Kano.
Daga karshen tattauna wacce ta sami halartatar manyan jamian Hisbah,, Babban kwamandan Hisbah ya ja kunnen matar ya kuma janyo hankalinta da ta ji tsoron Allah, ta kuma tabbatar da sahihancin Al amari kafin yada shi. Kamar yadda ta baiyana da bakinta a kasa.