Ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU ta ƙara yajin aiki da ta fara watanni biyar da suka gabata da wasu makonni hudu.
Idan zaa iya tunawa; malaman da ke yajin aikin sun rufe jami’o’in gwamnati ne a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyar aiki (MoA) da ɓangarorin biyu suka shigar a 2020.
Shugaban ASUU na ƙasa Farfesa Emmanuel Osodeke a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin, ya ce anɗauki matakin ƙara tsawaita yajin aikin ne domin baiwa gwamnatin tarayya damar shawo kan matsalolin
Rilwan Umar a raayin sa yace : ‘Dama kungiyar ASUU ta zama kungiyar ‘yan adawa koda yake mutane Basu gane bane Amma Shi munafurci ko badade zai tonu, yawancin shuwagabannin ASUU ‘yan Afenifere da tsurarin ‘yankungiyar Biafra
Halima Sharif kuma Bayan Mika lamarin ga buwayi gagaramisali cewa tayi Innalillahi wainna ilaihir rajiun’
Lawan mamman kuwa addua yayi da cewa’ ‘Allah kawo maslaha amen’